TSARIN BB + RSI (1)



Bollinger Band shahararriyar masarrafar ishara ce "technical indicator" wadda mutane ke amfani da ita a kasuwa. John Bollinger shine mutumin da ya samar da wannan masarrafa a shekarar 1980.

Manufar wadannan layuka guda uku da wannan masarrafa ke dauke da su itace baka bayanan hawa da saukar farashin kasuwa:

1. Layi dake a sama "upper band"
2. Layin dake a tsakiya "middle band"
3. Layin dake a kasa "lower band"

Layin dake a sama na ishara da hawan farashi yayin da layin dake a kasa ke nuna saukar farashi. Layin dake a tsakiya kuma na aiki a matsayin layi na kwance da ya raba bayanan ishara a tsakanin layukan guda biyu wato; na sama da na kasa domin nuna bambancin bangarorin "baseline".

Mutane na amfani da bayanan wannan masarrafa wajen kimanta halin rashin tabbas na kasuwa "volatility". Kuma wannan ne dalili na kasancewar wannan masarrafa a rukunin manhajojin 'volatility indicators'.

Bugu da kari, ana amfani da bayanan wannan masarrafa wajen gane lokutan da mutane suka fi saye ko sayar da kirifto "overbought & oversold". Yayin da farashi ya taba layin dake a sama, wannan na ishara da hali na sayarwa "selling", yayin da kuma farashi ya taba layin dake a kasa shike nuna hali na saye "buying".

Tazara ta muhalli "space" dake akwai tsakanin layin kasa, sama da na tsakiya shine ke bayyana rashin tabbas ko hawa da saukar farashi na kasuwa da ake kira 'volatility' a turance.

Layin dake a tsakiya na dauke da tsarin lissafi da ake amfani da shi wajen nazarin bayanan kirifto ta hanyar daukar tsaka-tsaki "average" na tsawon lokuta ashirin "20 period moving average". Layukan sama da na kasa kuma na aiki da '2 StdDev' a kasa da saman Moving Average dake a tsakiya. 'StdDev' ko 'standard deviation' dai wani ma'aunin kididdiga ne dake bayyana girman rashin tabbas din hawa ko saukar farashi "price volatility".

Yayin da kaga layukan sun buda a tsakanin su "widen", wannan na nufin akwai gagarumin hawa ko saukar farashi a kasuwa. Yayin da kuma farashi bai motsi, yana zaune a guri guda, layukan za su matsi juna "narrow" wanda ke nufin akwai karancin hawa ko saukar farashi sanadiyyar rashin cinikayya mai girma dake faruwa a wannan lokaci.

Kana iya yin amfani da tsarin mu'amala da kasuwa na tsawon sa'a guda ko sa'o'i hudu. Kana iya canzawa zuwa tsawon lokaci da ka ke so.

In Sha Allah zamu ci gaba!
Xem bản gốc
post-image
Trang này có thể chứa nội dung của bên thứ ba, được cung cấp chỉ nhằm mục đích thông tin (không phải là tuyên bố/bảo đảm) và không được coi là sự chứng thực cho quan điểm của Gate hoặc là lời khuyên về tài chính hoặc chuyên môn. Xem Tuyên bố từ chối trách nhiệm để biết chi tiết.
  • Phần thưởng
  • Bình luận
  • Đăng lại
  • Retweed
Bình luận
0/400
Không có bình luận
  • Ghim